DALILLAI DAGA AL-QUR’ANI DA SUNNAH
AKAN DAUKAKUWAR ALLAH (SWA) A SAMA
GABATARWA
Godiya
ta tabbata ga Allah, muna godemashi muna neman taimakonshi, Allah ya tsaremu
daga sharroran kawunanmu da miyagun ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai
batar dashi, wanda Allah ya batar babu mai shiryar dashi. Ina shaida babu abun
bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai, bashi da abokin tarayya. Kuma lalle Annabi
Muhammadu (SAW) bawan Allah ne, kuma manzon Allah ne.
Hakika
zance mafi gaskiya shine littafin Allah, shiriyar da take kadai itace shiriya,
itace shiriyar Muhammadu manzon Allah (SAW) dukkan sharri ya tattaru akan
bidi’a (kagaggun abubuwa) dukkan bidi’a (kagaggun abubuwa) batace. Bata kuwa
makomarta wuta ce.
Bayan
haka, Hakika akwai wata matsala a cikin wannan zamani namu. Wadda ke kokarin
haifar da gurbata akidar musulmi. Matsalar itace samun wadansu mutane suna yada
cewar Allah yana ko ina da zatinsa, da kuma masu neman kore samuwar Allah, da
cewarsu Allah bai sama, bai kasa, bai gabas, bai yamma, bai kudu, bai arewa,
bai cikin duniya, bai wajen duniya. Kaga wannan yanakokarin yace babu Allah
(SWT) ke nan baki daya.
Kasancewar
wannan matsala ta shafi Tauheedi ma’ana kadaita Allah shi kadai da bauta da
kuma kadaita shi da sunayanshi da Siffofinshi batare da kamantashi ko misaltawa
ba, to yana da kyau ko wane mutum yaginu akan akida ingantacciya, watau irin
akidar manzon Allah (SAW) da Sahabbansa da kuma wadanda suka biyo bayansu da
kyautatawa.
Hakika
wannan shi ne babban dalilin dayasa har nayi wannan Rubutu wanda nabaiwa taken (DALILLAI
DAGA AL-QUR’ANI DA SUNNAH AKAN DAUKAKUWAR ALLAH (SWA) A SAMA) da fatar wannan dan rubutu zai
anfanar da jama’ar musulmi, su fahimci wannan matsala matukar Fahimta tare da
sanin hujjoji daga Al’qur’ani mai girma da hadissan manzon Allah (SAW)
Ingantattu, a Karkashin fahimtar ‘yan mazan jiya watau magabatanmu na kwarai (Salafunassalih)
Daga
karshe Ina rokon Allah yasa Albarka acikin wannan aiki, kuma ya bani ladar aikin
tare da mahaifana da malamaina da dukkan musulmi, amin.
Abu-Abdurrahman
BASHIR
HASHIM TSANU
Zurmi
Local Gov’t Zamfara State, Nigeria.
08063109662,
08083213894
DALILLAI
DAGA AL-QUR’ANI DA SUNNAH AKAN DAUKAKUWAR ALLAH SUBIHANAHU WATA’ALA A SAMA
Hakika dalillan Al-qur’ani mai girma da sunnar
Annabi madaukakiya sun siffanta Allah Subihanahu wata’ala da daukakuwa a sama,
da kuma kasancewarsa birbishin komi, da kuma daidaituwarsa akan Al-arshi,
hakika akwai ayoyi da hadissai nau’o’a daban-daban masu yawa akan daukakuwar
Allah (SWT) a sama. Daga cikinsu akwai:-
BAYANI
KARARA AKAN DAUKAKUWAR ALLAH A SAMA (YANKE)
kuma wannan dalili ne akan dukkan matakai na daukakar zatin Allah da kudurarsa
da buwayarsa; yazo a gurare masu yawa daga ciki akwai
1.
Allah
madaukakin sarki yace “Ka tsarkake sunan Ubangijinka mafi
daukaka” (suratul
A’ala aya-1)
2.
Allah
(swt) yace “Alhali babu wani mai wata ni’ima
wurinsa wadda ake neman sakamakonta, face dai neman yardar ubangijinsa mafi
daukaka” (suratul
Lail, aya-19-20)
3.
Allah
(swt) yace “Shi ne masanin fake da bayyane, mai
girma, madaukaki” (suratur
Ra’ad, aya-9)
4.
Allah
(swt) yace “Kuma suka sanya wa Allah abokan
tarayya, Al’jannu, alhali kuwa (shi) ya halittasu, kuma sun kirkira masa diya
da ‘ya’ya, ba da ilmi ba, tsarkinsa ya tabbata, kuma ya daukaka daga abinda
suke siffantawa” (suratul
An’am, aya-100)
5.
Allah
(swt) yace “Kuma suna bautawa wanin Allah, abin
da baya cutar dasu kuma baya amfaninsu kuma suna cewa –‘Wadannan ne macetanmu a
wurin Allah’- kace –‘shin kuna baiwa Allah labari ne ga abinda bai sani ba, a
cikin sammai ko a cikin kasa? Tsarkinsa ya tabbata kuma ya daukaka daga abinda
duk suke yin shirki dashi” (suratu
Yunus. Aya-18)
6.
Allah
(swt) yace “Tsarkinsa ya tabbata kuma ya daukaka
daga abinda suke fada, daukaka mai girma” (suratul
Isra’I, aya 43)
7.
Allah
(swt) yace “Allah mamallakin gaskiya, ya daukaka,
babu abin bautawa, face shi. Shi ne ubangijin Al’arshi, mai girma” (suratul Muminun, aya-116)
8.
Allah
(swt) yace “Kuma lalle ne shi, girman ubangijinmu
ya daukaka, bai riki mata ba, kuma bai riki da ba” (suratul Jinni, aya-3)
9.
Allah
(swt) yace “Kursiyyunsa ya yalwaci sammai da
kasa. Kuma tsaresu baya nauyayarsa. Kuma shi ne madaukaki, mai girma” (suratul Baqara, aya-255)
10. Allah (swt) yace
“Wan can! Saboda lalle ne Allah, shi ne gaskiya, kuma lalle ne abin da suke
kira, waninsa, shi ne karya, kuma lalle ne Allah, shi ne madaukaki, mai girma” (suratul Hajji, aya-62)
11. Allah (swt) yace
“Kuma wani ceto baya anfani a wurinsa face fa, ga wanda yayi izni a gare shi,
har a lokacin da aka kuranye tsoro daga zukatansu, sai suce me ne ne
Ubangijinku yace? Suce ‘Gaskiya, kuma
shi ne madaukaki, mai girma” (Suratus
Saba’I, aya-23)
12. Allah (swt) yace
“Wancan Sababinsa, lalle (shine) idan an kirayi Allah shi kadai sai ku kafirta,
kuma idan akayi shirka game da shi, sai kuyi imani. To, hukuncinfa, na Allah
madaukaki, mai girma ne” (Suratul
Ghafir, aya-12)
13. Allah (swt) yace
“(Allah) shi ne da abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin kasa, kuma shi
ne madaukaki, mai girma” (Suratush
Shura, aya-4)
14. Allah (swt) yace
“Kuma baya kasan cewa ga wani mutun Allah ya yi masa Magana face da wahayi, ko
daga bayan wani shamaki, ko ya aiko wani manzo, sa’an nan ya yi wahayi, da
izninsa ga abin da yake so. Lalle shi, madaukaki ne mai hikima” (Suratush Shura, aya-51)
Dukkan
wadannan ayoyi sun fito da jawabi karara akan Daukakar Allah Subihanahu
wata’ala a sama yanke (kai tsaye), Daukakar kuwa ta kowace fuskar (ma’ana)
Zatinsa da kudurarsa da kuma buwayarsa.
BAYANI
KARARA AKAN DAIDAITUWA TARE DA GWAMATA DA HARAFIN ALA WANDA KE NUNA
KEBANTUWARSA KO DAUKAKARSA AKAN AL-ARSHI, WANDA YAKE SAMAN HALITTU
Kuma
mafi yawa Kalmar Istiwa’u ta kanzo da harafin ( )
“Summa” amma tana Shiryarwa ne ga jerantawa da jinkirtawa, shi ne Siyakin
yanke. A cikin ma’anarsa wanda abokin Magana baya daukar wata ma’ana ta daban.
1.
Allah
madaukakin Sarki yace “Lalle ne Ubangijinka Allah ne, wanda
ya halitta sama da kasa a cikin kwanaki shidda, sa’annan kuma ya daidaita akan
Al-arshi, yana sanya dare ya rufe yini yana nemansa da gaggawa, kuma rana da
wata da taurari horarru ne da Umurninsa. To shi ne da halittar kuma da umurnin.
Albarkar Allah ubangijin halittu ta bayyana” (Suratul
A’araf, aya-54)
2.
Allah
(swt) yace “Allah ne Ubangijinku wanda ya halicci
sammai da kasa a cikin kwanaki shidda, sannan kuma ya daidaita akan Al-arshi
yana gudanar da al-amari. Babu wani maceci face a bayan izninsa, wannan ne
Allah, Ubangijinku, sai ku bauta masa, shin fa, baku tunani” (Suratu Yunus, aya-3)
3.
Allah
(swt) yace “Allah shi ne wanda ya daukaka sammai,
ba da ginshikai ba wadanda kuke ganinsu, sa’an nan kuma ya daidaita akan
Al-arshi kuma yahore rana da wata, ko wane yana gudana zuwa ga ajali ambatacce.
Yana shirya al-amari, yana rarraba ayoyi daki-daki mai yiyuwa ne ku yi yakini
da haduwa da Ubangijinku” (Suratur
Ra’ad, aya-2)
4.
Allah
(swt) yace “Allah mai Rahama ya daidaita kan
Al-arshi” (Suratu
D.H, aya-5)
5.
Allah
( yace “Wanda ya halitta sammai da kasa da abin da yake a
tsakaninsu, a cikin kwanuka shidda, sa’an nan ya daidaita a kan Al-arshi, mai
rahama, sai ka tambayi mai bayar da labari game da shi” (Suratul Furqan, aya-59)
6.
Allah
(swt) yace “Allah ne wanda ya halitta sammai da
kasa da abin da yake a tsakaninsu a cikin kwanuka shidda sa’an nan ya daidaita
akan Al-arshi. Ba kuda baicin shi, wani majibinci, kuma babu wani maceci. Shin
ba zakuyi tunani ba” (Suratus
Sajada, aya-4)
7.
Allah
(swt) yace “Shi ne wanda ya halitta sammai da
kasa a cikin wasu Kwanuka shidda, sa’an nan ya daidaita akan Al-arshi, yana
sanin abinda ke shiga cikin kasa da abin da ke sauka daga sama da abinda ke
hawa cikinta, kuma Alhali mai gani ne ga abinda kuke aikatawa” (Suratul Hadid, aya-4)
Wadannan
ayoyi dukkaninsu suna tabbatar da daukakar Allah (SWT) da kuma kasan cewarsa a
kan birbishin komi. Kuma ma’anar Kalmar “ISTAWA” a harshen larabci, idan akayi
ta’addinta da “ALA” tana nufin daukaka da kuma daukakuwa. Saboda haka ne
tafsiran magabata basu fitar da wannan lafazinba daga cikin ibarori guda hudu,
wadanda Al-allamatu Ibnul Qayyum ya kawo a cikin littafinsa (Nuniyya, a shafi
na-67-68) Ibarorin kuwa sune “(1) Istaqarra, (2) Ala, (3) Irtafa’a, da kuma (4)
Sa’ida” duk wadannan suna nuna daukakuwar Allah (swt) Akan Al-arshi.
Haka
kuma su magabata suna fasara “Istiwa’I” ne da daukakuwa akan Al-arshi kamar
yanda Imamul Bukhari yace a cikin littafinsa Sahihul Bukhari, Daga Abil A’liya
yana cewa dangane da fadar Allah (SWT) “Summastawa Alal Arshi” sai yace
daukakuwa (Sahihul Bukhari a kitabut Tauheed, babina 22 wakana Arshuhu alal
ma’u)
BAYAR
DA LABARIN DA ALLAH SUBIHANAHU WATA’ALA YAYI AKAN HAWAR DA ABUBUWA DA TAFIYAR
DASU DA DAUKAKASU SAMA ZUWA GARESHI
1.
Allah
madaukakin sarki yace “Wanda yakasance yana neman wata izza,
to Allah ne da izza gaba daya zuwa gareshi Magana mai dadi ke hawa, kuma aiki
nakwarai yana daukarta, kuma wadanda ke yin makircin munanan ayyuka, suna da
wata azaba mai tsanani, kuma makircin wadannan yana yin tasgoro” (Suratu fadir, ayata-10)
2.
Allah
(swt) yace “A’a Allah ya dauke shi zuwa gare shi,
kuma Allah ya kasance mabuwayi mai hikima” (suratun
Nisa’I, aya-158)
3.
Allah
(swt) yace “A lokacin da Ubangiji yace; ya Isa!
Lalle ni mai karbar ranka ne, mai daukaka ka zuwa gareni. kuma mai tsarkakeka
daga wadanda suka kafirta…..”(Suratu
Al’Imran, ayata 55)
4.
Allah
(swt) yace “Yana shirya al-amari daga sama zuwa
ga kasa, sa’an nan ya taka zuwa gare shi a cikin yini wanda gwargwadonsa
shekaru dubu ne ga abinda kuke lissafawa” (suratus
sajada, aya-5)
5.
Allah
(swt) yace “Daga Allah mai matakala, Mala’iku da
Ruhi (Jibrila) suna takawa zuwa gare shi a cikin yini wanda gwargwadonsa,
shekara dubu hamsin ne” (suratul
ma’aa’rij, aya-3,4)
6.
An
karbo daga Abi Huraira (R.A) hakika
manzon Allah (SAW) yace “mala’iku suna bibiya a cikinku da
dare da kuma mala’ikun rana kuma suna haduwa a sallar la’asar da sallar asuba,
sannan wadanda suka kwana cikinku su hau (sama) sai (Allah) ya tambayesu kuma
shi (Allah) ya fisu sani. Sai yace, yaya kuka baro bayi na? sai suce mun barsu
suna sallah kuma mun same su suna sallah” (Sahihul
Bukhari a kitubuttauheed hadisi na-7429)
7.
An
karbo daga Abi Huraira (RA) yace manzon Allah (SAW) yace
“Duk wanda yayi sadaka da kwatankwacin dabino daga abunda ya nema na halas.
Babu abunda yake hawa gurin Allah sai abu mai tsalki Lallai Allah madaukakin
sarki yana karbarta da hannunsa na dama, sannan ya reneta ga ma’abucinta, kamar
yanda dayanku yake renon kwaya har tazama kamar dutse” (Duba Sahihul Bukhari a
kitabuttauheed hadisi na-7430).
8. An karbo daga Abu Musal Ash’ari (RA)
yace manzon Allah ya mike tsaye a cikinmu da kalmomi guda biyar; sai yace
“Lalle Allah baya barci, kuma baya kamata gareshi yayi barci, kuma yana saukar
da adalci kuma yana daukakashi. Ana daukaka ayyukan dare zuwa gare shi (Sama)
kafin ayyukan rana, da ayyukan rana kafin ayyukan dare abunda ya shamakance
Allah shine haske, da zai yaye shi (hasken) da
Hasken Fuskarsa ya kona duk inda haskensa ya kai daga halinttunsa. (Duba Sahihu Muslim, Kitabul
Al’iman, Hadisi na-85)
9.
An
karbo daga Abi Huraira (RA) yace manzon Allah (SAW) yace
“Ina Rantsuwa da wanda rayuwata take hannunsa anyo kusa da a saukar da Dan
Maryam a cikinku yana mai hukunci mai adalci, ya karya (cross) kuma ya kashe
Alade, kuma ya dora jiziya (haraji) kuma ya raba dukiya har sai an kai babu
mutun daya dake bukata. Har sujjada daya ta kasance tafi zama Alheri daga
duniya da abunda ke cikinta” (Duba Sahihul Bukhari a kitabu
Ahadisul Anbiya a babin Nuzulul Isah Bin
Maryam (as) hadisi na-3448)
10. kuma wannan hadisi shaheed ne da
kuma fasara game da fadar Allah (swt) cewa “A’a Allah ya dauke shi zuwa gare shi,
kuma Allah ya kasance mabuwayi mai hikima”
(suratun Nisa’I, aya 158)
Haka
kuma Kissar Mi’irajinsa Sallallahu Alaihi wasallam da kuma bada labarinsa cewa
yana kai da komowa tsakanin Annabi Musa (as) da Ubangijinsa a daren Mi’iraji,
saboda arage masa yawan salloli. Sai yahau zuwa ga Ubangiji kuma ya dawo gurin
Musa (as) sau da yawa (Duba Sahihul Bukhari a kitabussalah Babin Kaifa
furidatussalati fil isra’I hadisi na-349)
BAYANI
KARARA AKAN SAUKAR AL’QUR’ANI MAI KIRMA DAGA ALLAH (SWT)
1.
Allah
madaukakin sarki yace “Kace, Ruhul Kudusi ne ya sassaukar
dashi, daga Ubangijinka da gaskiya domin ya tabbatar da wadanda suka yi imani,
kuma (domin) shiriya da bushara ga Musulmi” (Suratun
Nahli, aya-102)
2.
Allah
(swt)yace “Saukar da Littafin daga Allah ne
mabuwayi masani” (Suratul
Ghafir, aya-2)
3.
Allah
(swt) yace “Saukar daga Allah ne, mai Rahama mai
jinkai” (Suratul
Fussilat, aya-2)
4.
Allah
(swt) yace “Barna bazata je masaba daga gaba
gareshi ba, kuma bazataje daga bayanshi ba, Saukakkene daga mai hikima abun
godiya”
(Suratul Fussilat, aya-42)
Wadannan
dalillai ne akan daukakar Allah saman halittunsa, domin harafin ( ) (daga) a cikin wadannan ayoyin don kai
matukar ma’anar daukakar Allah (swt) kuma sauka ko saukarwa bata kasancewa sai
daga wanda yake sama.
BAYANI
KARARA CEWA ALLAH (SWT) YANA SAMA
1.
Allah
mai girma da daukaka yace “Shin ko kun amince cewa wanda ke sama,
ba zai iya shafe kasa tare da ku ba, sai gata tana mai girgiza. Ko kun amince
cewa wanda ke sama ba zai iya sako muku iskar guguwa ba? To, zaku san yadda
(akibar) gargadi na take”
(suratul Mulk, aya-16-17)
Fassama’u
suna ne na jinsi ga daukaka ga dukkan abinda ke sama, kamar; Sammai, Kursiyyu
da kuma Al’arshi. Saboda haka, cewar Allah (swt) ( ) Yana
nufin ai birbishin sama ba a kasa ba.
Kasancewar
Allah (swt) yana sama baya nuna cewa yana cikin wani abu wanda yake samamme,
kuma wanda yakewayeshi domin babu wani abu samamme saman halittu wanda ba
(Allah) ba. Haka kuma idan mukace Al’arshi yana cikin sama baya nuna yana cikin
wani abu samamme wanda yakewayeshi. Shi Allah (swt) shi ne Madaukaki, wanda ke
saman halittu duka, shi ne kuma saman Al’arshinsa wanda ba wani abu acan wanda
bashiba.
Kuma
idan muka kaddara abunda ake nufi da sama acikin wadannan nassosa wannan samar
ginanniya (watau sammai). To sai muce ma’anar Kalmar ( ) tana nufin (
) watau saman (ba wai ciki ba) kamar cewar
Allah madaukakin sarki “Saboda haka kuyi tafiya a cikin kasa wata hudu……” (Suratut
Tauba, aya-2) ma’anar acikin kasa tana nufin saman kasa, domin ba’ayin tafiya
cikin kasa sai dai saman ta.
2.
Haka
kuma Allah (swt) yace “…….kuma Lalle zan tsire ku a cikin
kututturen itacen dabino, kuma lalle zaku sani wanenmu ne mafi tsananin azaba,
kuma wane ne mafi wanzuwar (azaba)” (suratu
D.H, aya-71) anan ma’anar Kalmar “a cikin kututturen itacen dabino…) shi ne a jikin kututturen itacen
dabino.
3.
Akwai
hadisi wanda shima yana karfafa maganar Allah (swt) ( acikin sama) manzon Allah (saw) yace “Shin
bazaku amince mani ba, kuma ni amintacce ne daga wanda ke cikin sama, labarin
sama yana zomani safe da marece” (sahihul Bukhari a kitabul Migaza).
BAYANI
KARARA DA KEBANCE WASU HALITTU CEWA SUNA GURINSA SUBIHANAHU WATA’ALA; Kuma wasunsu sunfi wasu kusanci
dashi, da kuma tambayar da manzon Allah(saw) yayi da Kalmar ( A’ina) wadannan dalillai ne akan
cewa Allah (swt) baya ko wane guri da
zatinsa, sai dai yana sama akan halittunsa.
1.
Allah
maigirma da daukaka yace “Lalle ne, wadanda ke wurin Ubangijinka,
ba su yin girman kai ga bauta masa, kuma suna tsarkake shi da tasbihi. Kuma a
gareshi suke yin sujuda” (Suratul
A’araf, aya-206)
2.
Allah
(swt) yace “Kuma shi ne da mallakar wanda yake a
cikin sammai da kasa kuma wadanda suke wurinsa (watau mala’iku), basu yin
girman kai ga ibadarsa, kuma basu gajiya” (Suratul
Anbiya, aya-19)
3.
Allah
(swt) yace “To idan sun yi girman kai, to wadanda
ke a wurin Ubangijinka, suna tasbihi a gare shi, a dare da rana, alhali kuwa
su, basu kosawa” (Suratu
Fussilat, aya-38)
4.
An
karbo daga Abi Huraira (RA) daga Annabi (saw) yace
“Lalle Allah, lokacin da ya kare halittu sai ya rubuta a wurinsa, saman
Al’arshinsa, cewa Rahamata ta gabaci hushina”
(Duba Sahihul Bukhari a kitabuttauheed, hadisi na-7422)
5.
Haka
kuma tambayarsa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, ga wata yarinya
inda yacemata “A’ina Allah yake?” sai tace a sama yake, sai yace “To
ni wanene?”
sai tace kai manzon Allah ne, sai yace “inta ta Muminace” (Duba Sahihu Muslim a kitabul Masa-jeedbabun
Naskhul kalami fis-salati hadisi na 333)
BAYANI
KARARA AKAN KASANCEWARSA SUBIHANAHU WATA’ALA BIRBISHIN KOMI
1.
Allah
Maigirma da daukaka yace “Suna tsoron Ubangijinsu daga bisansu,
kuma suna aikata abinda ake Umurninsu” (Suratun
Nahl, aya-50)
2.
Allah
(swt) yace “Kuma shi ne tankwasa a kan bayinsa
kuma shi ne mai hikima, masani”
(Suratul An’am, aya-61)
BAYANI
KARARA AKAN SAUKOWARSA SUBIHANAHU WATA’ALA A CIKIN KOWANE DARE ZUWA SAMAN
DUNIYA:-Abun
sani ne ga dukkanin al’umma cewa sauka bazata kasance ba sai daga Sama zuwa
kasa.
1.
Yazo
a cikin hadisin Abi Huraira (RA) manzon Allah (saw) yace “Ubangijinmu
mai girma da buwaya yana saukowa a cikin ko wane dare zuwa saman duniya,
lokacin da kashi daya bisa ukkun dare na karshe ya yi saura, sai yace, wa ne ne
ke rokona in karba masa, wa ne ne ke tambayata in bashi wa ne ne ke neman
gafarata in gafarta mashi”
(Duba Sahihul Bukhari a Kitabussah a Babin Addu’a’I, Wassalati min
Akhiril-laili. Hadisi na-1145).
ISHARA
(NUNI) DA DAN YATSA CEWA ALLAH (SWA) YANA SAMA;-Kamar yanda manzon Allah (saw)
yayi Ishara (Nuni) dadan yatsansa lokacin hajjin bankwana, a gaban jama’a masu
yawa.
1.
Manzon
Allah yace “Ku ababen tambaya ne a kaina mi zaku
fada? Sai suka ce munshaida cewa kai ka isar, kuma ka Bayar, kuma kayi nasiha.
Sannan sai manzon Allah yace da dan yatsansa manuni yana daga shi zuwa sama
yana nuna shi ga mutane “Allah ka shaida, Allah ka shaida, Allah ka shaida” (Duba Sahihu Muslim Kitabul Hajji,
babin Fi-hajjatun Nabiyi (saw) hadisi na-707)
BAYAR
DA LABARINSA SUBIHANAHU WATA’ALA GAME DA FIR’AUNA;- Cewa Fir’auna ya gina bene domin
yahau zuwa ga Ubangijin Musa (AS) domin ya karyata Annabi Musa (AS) dangane da
labarin da yabashi cewa lalle Ubangiji Maigirma da daukaka yana Saman sammai;
sai Fir’auna yace “……Ya hamana! Ka gina mini bene,
tsammanina zan isa ga kofofi. Kofofin sammai, domin in yi tsinkaya zuwa ga abin
bautawar Musa, kuma lalle ni, hakika, ina zatonsa makaryaci……” (Suratul Ghafir, aya-36, 37) sai
Fir’auna ya karyata Annabi Musa (AS) dangane da labarin da yabashi cewa
Ubangijinsa Allah yana saman sama (Duba Littafin I’ilamul muwakki’ina An-Rabbil
A-lamina na Ibni Kudama 2/302).
Idan
mun lura da duk wadannan ayoyi bayyanannu da hadissai ingantattu, zamu fahimci
cewa Allah Subihanahu Wata’ala ya siffantu da Daukaka da kasancewarsa birbishin
komi, da kuma kasancewarsa saman dukkan halittunsa. Kuma babu wani mutum mai hankali
wanda zai fahimci wani abu sabanin wannan. Alhamdu-lillahi
RUFEWA
Mai
karatu yana da kyau ka fahimci cewa ita dai akidar korewa Allah (swa)
Siffofinsa da kuma akidar masu tabbatar da wasu siffofin Allah (swa) kuma su
kore wasu siffofin. Akida ce wadda ta samo asali ne daga bangarori guda biyu,
bangarorin kuwa sune Jahamiya da kuma Asha’ira.
Akidar
Jahamiya:-
An samo wannan akidar ne daga daliban yahudawa da mush-rikai, da kuma batar
masu ta’asubanci. Mutum na farko da yace “Na sani a hakika Allah (swa) ba akan
al’arshi yake ba” sai yace abunda ake nufi da Kalmar (Istawa) ‘Dai-daituwa’ tana
nufin (Istaula) watau mamaya, kamar ka mamaye abunda yake ba can ba mallakarka
bane. Wannan mutum shine Ja’adu dan Darham, kuma ya karbi wannan akidar ne
gurin malaminsa Jaham Dan Safwan, daga nan ne sai aka sami asalin wannan
mummunar akidar ta bata. Daga karshe dai an kashe shi Ja’adu din a kasar Iraki
a cikin shekara ta 118 bayan hij’rar manzon Allah (saw) daga makka zuwa madina.
Ya
dan uwa mai karatu kasani cewa wannan akidar ta fito ne daga hannun al’majiran
mush-rikai da masu ta’asubanci da yahudawa, to tayaya zukatan muminai da duk
wani mai lafiyayyen hankali zasu sami natsuwa tahanyar yin riko da maganganun
wadanda Allah yayi hushi dasu watau yahudu da nasara, kuma ace mumini ya bar
hanyar wadanda Allah yayi Ni’ima agaresu daga cikin Annabawa da masu gaskiya da
shahidai da nagartattun bayinsa. Hakika duk wani mumini da kuma duk wani mai
cikakken hankali bazai bar hanyar bayin Allah na gari ba ya kama hanyar
batattu.
Akidar
Ash’ariya (Ash’ariyanci):-
Sune mabiya Al-allama abul-Hassan Aliyu bin Isma’ila bini abi Bashar
Al-ash’ari. Wani malami ne daga cikin malaman karni na ukku bayan hijirar
manzon Allah (saw) daga makka zuwa madina.
Wannan
malami afarkon al-amarinsa yana kan akidar Mu’utazilanci, Mu’utazilanci kuwa
wata kungiyace daga cikin kungiyoyin da suke jingina kansu zuwa ga musulunci.
Amma sun sabawa al’ummar musulmi a cikin wadansu matsaloli na akida watau
Tauheedi, Kamar matsalar ganin Allah a ranar al’kiyama, da matsalar yin ceto,
kuma suna korewa Allah duk siffofinsa. To shi Abul-Hassan Al’ash’ari ya kasance
acikin wannan akidar ta mu’utazilanci har tsawon shekaru Arba’in (40) daga nan
saiya bar wannan akidar ta Mu’utazilawa amma kuma bai dawo akidar Ahlussunnati
wal’jama’a ba a wannan matsayin ne sai shi Abul-Hassan Al-ash’ari ya tabbatarwa
da Allah siffofi guda bakwai, wadanda hankalinsa ya yarda dasu. Siffofin kuwa
sune; 1. As-sam’u, 2. Al-basaru, 3. Al-ilmu, 4. Al-hayatu, 5. Al-iradatu, 6. Al-baka’u
da kuma 7. Al-kalamu.
Bayan
ya yarda da wadannan siffofi guda bakwai sai kuma ya dinga bin sauran siffofin
Allah (swa) yana yimusu tawili. Amma daga baya yabar wannan akidar ta dalilin
irin bincikensa da yakeyi, ya dawo akan akidar Ahlussunnati wal’jama’a ya daina
yin tawili a cikin siffofin Allah (swa) kuma ya tabbatar da dukkanin siffofin
Allah (swa). Babban abunda zai tabbatar mana da cewa Abul-Hassan Al’ash’ari yabar
bin waccen akidar tasa ya dawo akan akidar Ahlussunnati wal’jama’a shi ne
littafansa guda biyu wadanda ya rubutasu dakansa bayan yabar waccen akidar
tasa, littafan sune; (Al-Ibana An Usuluddiyana da kuma littafin Makalatul
Islamiyin…..) yan uwa idan muka duba wadannan littafai zamuga irin yanda ya
shinfida akidar Ahlussunnati wal-jama’a tsantsa, ya yarda da dukkanin siffofin
Allah (swa) batare da tawili ba.
To
lokacin da yake akan waccen akidar ma’ana yabar Mu’utazilanci kuma bai dawo kan
akidar Ahlussunnati wal’jama’a ba. To wannan matsayin shi ake kira da akidar
ASH’ARIYANCI. Dalili kuwa shi ne, alokacin shi ba akan akidar Mu’utazilawaba
kuma ba akan akidar Ahlussunnati Wal’jama’a ba. Kenan yana kan wata akida
sabuwa takansa. Kuma shi ne dalilin dayasa ake dangana masa wannan akida ta
Ash’ariyanci. Mai karatu kariga kaji cewa shi Abul-Hassan Al-ash’ari Wanda ake
dangana akidar zuwa garesa ya bar wannan akidar tun yana da rayuwa kafin ya
mutu.
Ina
fatar wadannan ayoyi masu tsalki da Hadissan Annabi Madaukaka da kuma jawaban
da suka gabata zasu gamsar da duk wani mutum wanda yake dashubuha ko kuma kishirwar
sanin wannan matsala zai samu cikakkiyar fahimta tare da samun ingantattun
hujjoji, Allah mudace Amin.
Daga
karshe Ina sanar da malamaina da yan uwa daliban ilimi cewa kofofina suna nan a
bude domin karbar gyara da kuma shawarwari, 08063109662 bashirhashimu@yahoo.com
Ina
shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Ina Neman gafararka, ina tuba
zuwa gareka.
BASHIR
HASHIM
Ramadan
09/09/1433 AH 28/07/2012
DON ALLAH KAYI SHARING DIN WANNAN PAGE DIN GA 'YAN UWA MUSULMI
DON ALLAH KAYI SHARING DIN WANNAN PAGE DIN GA 'YAN UWA MUSULMI